Ronaldo bai san komai ba game da harkar kwallo idan aka kwatanta shi da Messi in ji Rodri
Dan wasan tsakiya na Manchester City, ya yi kakkusar suka ga Cristiano Ronaldo inda yace dan wasan ba shi da hazaka idan aka kwatanta da Lionel Messi.
Rodri, wanda ke murmurewa daga tiyatar da aka yi masa a guiwa, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi a shirin gidan talabijin na kasar Spain.
Ya ce, “Lionel Messi dan wasa ne mafi girma a kowane lokaci ba tare da kokwanto ba kuma Cristiano Ronaldo ya yi nasarar daidaita kan sa da shi amma mu da muka yi wasa da su muna iya ganin bambanci a tsakanin su.