Rikicin manoma da makiyaya a Nasarawa ya yi ajalin mutum 3


Akalla mutum uku ne suka rigamu gidan gaskiya, sakamakon wani sabon rikici da ya faru tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Toto jihar Nasarawa.

Kwamishinan yan sandan jihar Umar Nadada, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rikicin ya faru ne a wani gari mai suna Dogon Dutse da ke tsakanin kananan hukumomin Nasarawa da Toto.

Ya ce rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin ne ranar litinin da misalin karfe 4:30pm, bayan da jami'ai suka isa wurin sun tarar da mutum biyu sun mutu inda hudu suka samu raunukka.

A cewar kwamishinan, daga baya an gano gawar mutum daya a cikin daji kuma yanzu haka suna gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp