Kamfanin mai na Nijeriya NNPCL ya ce ya daina shigowa da tataccen mai a cikin kasar, a yanzu yana sayen mai ne daga matatar Dangote da kuma wasu matatun mai na cikin gida.
Shugaban Kamfanin Mele Kyari ne ya sanar da hakan a jiya yayin wani taro kan albarkatun mai da aka gudanar a Lagos.
Duk da cewa Nijeriya na daya daga cikin kasashen da ke fitar da danyen mai zuwa kasuwar duniya, shekaru da dama tana shigowa da mai wanda aka tace daga waje, saboda rashin matatar mai dake aiki a kasar.
Da yake jawabi, Mele Kyari yace a yanzu kamfanin mai ba ya shigowa da fetur daga kasashen waje, kuma ya karyata zargin yi wa matatar mai ta Dangote zagon kasa.