Yan wasan Super Eagles sun samu tikitin zuwa kasar Morocco domin buga gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka ta shekara ta 2025.
Super Eagles ta samun wannan nasara bayan da su ka tashi 1 - 1 a wasan karshe da ta buga da kasar Benin.
Duk da cewa akwai wasa daya da ta rage wa 'yan wasan, Nijeriya ce kan teburi a rukuni na 'D' da maki 11, yayin da Benin ke bi ma ta da maki 7, Rwanda kuwa maki 5.