Gwamnatin tarayya ta samu lamuni na dala miliyan dari da talatin da hudu (dala miliyan 134) daga bankin raya Afirka (AfDB) domin bunkasa noman iri da hatsi a kasar.
Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da ayyukan noman rani na shekarar 2024/2025 a Calabar, Cross River.
Manufar ita ce a tabbatar da cewa kasar ta samu dogaro da kanta a cikin muhimman kayan amfanin gona irin su alkama, shinkafa, masara, dawa, waken soya, da rogo.