Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya ya bayyana cewa an kashe biliyan 8.8 wajen gyara turakun lantarki da 'yan bindiga da wasu bata gari su ka lalata a wurare daban-daban a fadin kasar nan.
Manajan daraktan kamfanin Injiniya Suleiman Abdulaziz ne ya sanar da hakan a Abuja, inda ya ce daga 13 ga watan Janairun 2024 zuwa yanzu manyan turakun lantarki 128 ne aka lalata.
Injiniya Suleiman ya nuna damuwarsa cewa duk lokacin da a ka cafke wadanda ke wannan aika-aikar ana gurfanar da su akan laifin sata a maimakon lalata kayan gwamnati, abinda ke sa ana bayar da su beli daga baya.
Category
Labarai