Ministan lafiya Farfesa Muhammad Pate ya ce a kowace shekara Nijeriya na asarar makudan kudaden da suka kai dala biliyan 1.1 saboda cutar malaria.
Da yake jawabi a lokacin taron kwamitin yaki da cutar malaria karo na farko da ya gudana a Abuja, Ministan ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin sarakuna da malamai domin kawar da cutar.
Wata sanarwa da mataimakin kakakin ma'aikatar lafiya ya fitar, ta ambato Farfesa Pate na cewa cutar zazzaɓin cizon sauro babbar barazana ce ga harkar lafiya, tattalin arziki da kuma ci gaban kasa.
Category
Labarai