Na tarar da mataccen jemage a bisa gadon da nake kwana kafin hukumar zaben INEC ta ayyana ni matsayin Gwamnan jihar Edo - Okpebholo
Gwamna Okpebholo na ya Jihar Edo ya bayyana cewa ya tarar da mataccen jemage a bisa gadon da ya ke kwana kafin hukumar zabe ta ayyana shi a matsayin gwamna.
Gwamnan yace shi kam ya mika lamurransa ga Allah ne, a lokacin da abokan takararsa ke bin hanyoyi daban daban domin suga su suka yi nasara.
Okpebholo ya fadi haka ne a lokacin wani biki da aka shirya bayan rantsar da shi a filin wasa na Dr Samuel Ogbemudia dake Benin, babban birnin jihar Edo.