Na san wadanda suka sa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta yi bincikena in ji wanda ya yi wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban kasa, Okowa


Tsohon Gwamnan jihar Delta Dr. Ifeanyi Okowa, ya ce ba ya jin tsoron binciken da hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ke yi masa, saboda ya san mutanen da ke da hannu a binciken.

Okowa wanda shi ne tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekara ta 2023, ya ce dukkanin zarge-zargen da ake masa saboda siyasa ne.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ga shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Delta Manjo Janar Felix Mujakperuo mai ritaya, a gidan sa da ke birnin Asaba na jihar.

Hukumar EFCC na gudanar da binciken tsohon gwamnan akan zargin karkatar da kudaden da suka kai naira tiriliyan 1.3

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp