Fashewar wata mota dauke tukunyar gas a kauyen Magana dake karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina ta jikkata mutane da dama tare da lalata motoci da gidaje.
Shaidu sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a wani wurin sayar da iskar gas ta girki, wanda ake zargin an ajiye kayan da aka safararsu daga Jamhuriyar Nijar, a cewar rahoton Dailytrust.
Jami’in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da cewa ba a samu hasara rayuwa ba sai dai motoci 6 ne suka lalace sanadiyar fashewar.