Matsin rayuwa: yanzu 'yan Nijeriya bashi su ke ci ko su haƙura da cin abinci - hukumar NBS


Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce karamcin cimaka da matsalar tsaro da hauhawar farashin kayayyaki ya tilastawa gidaje da dama rage sayayyar da suke yi. 

Binciken da hukumar ta gudanar tare da bankin duniya, ya nuna cewa kashi 65 cikin dari na iyali basu samun abinci lafiyayye saboda rashin kudi. 


Hukumar ta ce lamarin ya yi kamari ne a watannin Yuli, Yuni da Augustan 2024, kuma ta alakanta hakan ga karamcin abinci wanda ya jefa ahali sama da rabin miliyan daya cikin wani hali. 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp