Tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali wajen inganta walwalar ‘yan Nijeriya a daidai lokacin da kasar ke fama da matsin tattalin arziki.
Osinbajo ya bayyana hakan ne a wani taron mata yan kasuwa na shekarar 2024 da aka gudanar a Abuja babban birnin Nijeriya.
'Yan Nijeriya dai na ci gaba da fuskantar matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a fadin kasar da ma matsalar karyewar darajar Na
ira