Matawalle ya isa birnin Riyadh na Saudiyya wajen babban taron tsaro na kungiyar IMCTC

 


Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya Bello Matawalle ya isa birnin Riyadh na Saudiyya inda zai gana da Yariman kasar Mohammed bin Salman, a wani bangare na halatar taron kungiyar kasashen Musulmai da ke yaki da 'yan ta'adda , IMCTC.


A yayin ziyarar aikin ministan ke yi a Saudiyya ya ziyarci hedikwatar kawancen kasashen Musulmi domin yaki da ta'addanci, inda ya yi godiya ga Sakatare Janar na kungiyar ta IMCTC, bisa gudunmuwar da suke bai wa Nijeriya ta hanyar horas da sojojinta dubarun yaki da ta'addanci.






Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp