Matatar mai ta gwamnatin Nijeriya da ke jihar Rivers ta soma aiki bayan daukar tsawon lokaci ana aikin zamanantar da ita.
Mai magana da yawun kamfanin mai na kasa NNPCL Femi Soneye, shine ya tabbatar da hakan.
Yayinda a ka fara daukar mai domin fita da shi daga matatar Fatakwal a yau Talata, Soneye ya ce NNPCL na aiki tukuru domin ganin cewa matatar Warri ta soma aiki itama.
Category
Labarai