Gwamnan Sokoto da Hamdiyya
Matashiya yar jihar Sokoto, Hamdiyya Sidi, wadda ‘yan sanda ke tuhumarta da furta wasu kalamai na tunzura jama’a, ta nemi gafarar gwamnan jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu.
Hamdiyya ta nemi afuwar ne a cikin wani takaitaccen bidiyo da ta saki a dandalin sada zumunta, inda ta ce "Ni ce wadda na yi furuci a kwanaki na yi batanci ga gwamna kan tsaro don haka ina neman afuwa" in ji Hamdiyya
Category
Labarai