Uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu ta musanta bayanan da ke cewa za ta jagoranci addu’o’in da za yi wa kasa kan halin da Nijeriya ke ciki.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Busola Kukoyi ya fitar, Remi Tinubu, ta ce a matsayinta na Kirista ta yi imani da addu’a amma akwai bukatar a tsara yin addua yadda ya kamata, tana mai cewa hakkin kowane dan Nijeriya ya yi wa kasa addua ba ita kadai ba.