Masu yiwa kasa hidima na NYSC sun yi kira da a aiwatar masu da sabon tsarin alawus na N77,000


Matasa masu yi wa kasa hidima sun yi kira ga gwamnatin shugaba Tinubu da ta aiwatar da sabon alawus na Naira 77,000 da ta sanar da shirin ba su a kwanakin baya. Matasan sun ce gaggawar fara aiwatar da sabon alawus din zai rage masu wahalhalun da suke ciki.

Jaridar Daily Nigerian ta ce duk da sanarwar gwamnatin Nijeriya ta watan Yulin 2024, amma har yanzu masu bautar kasar sun shaida mata cewa ana biyan su da tsohon alawus na N33,000 a duk wata.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp