Masu hakar ma'adinai 22 ne suka rasa rayukansu sakamakon ruftowar kasa a jihohin Adamawa da Taraba

Masu hakar zinare


Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 22 ne ake kyautata zaton sun rasa rayukansu sakamakon ruftowar kasa da ake hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, wanda ke cikin wani gandun daji na kasa da ya kai karamar hukumar Gashaka a jihar Taraba da kuma karamar hukumar Toungo a jihar Adamawa.


Adamu Jamtare, wani mai hakar ma’adinai daga Gashaka, ya bayyana cewa da yawa daga cikin wadanda suka rasu sun fito ne daga garin Jamtare da ke karamar hukumar Gashaka ta jihar Taraba.


Ya ce suna hakar zinare ne a wani yanki da ake kira Buffa zone a cikin wani gandun dajin Gashaka-Gumti, wanda tsayin sa ya mamaye sassan Gashaka da Toungo kuma dukkan masu hakar ma’adinai 22 da suka makale a cikin ramin ana kyautata zaton sun mutu.


Shugaban karamar hukumar Toungo ta jihar Adamawa, Injiniya Suleiman Toungo, ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin masu hakar ma’adanai 5,duk da cewa bai da tabbas kan adadin wadanda ke cikin ramin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp