Masu garkuwa da mutane da suka dauke yara 4 a jihar Kaduna sun tuntubi mahaifin yaran tare da neman naira miliyan 300 a matsayin kudin fansa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sun yi barazanar kashe karamin yaron dan shekaru biyu saboda kukan da yake yi.
Mahaifin yaran wanda ke zaune a Keke A, karamar hukumar Chikun, ya ce lokacin da suka kira shi yana ji lokacin da suke dukan yaran, ba yadda zai yi.
Yan bindigar sun sace yaran ne a lokacin da mahaifinsu ya ce asibiti domin duba mahaifiyarsu wadda aka kwantar da ita saboda rashin lafiya.
Category
Labarai