Shugaban hukumar da ke yaki da cuta mai karya garkuwa jiki a Nijeriya Dr Temitope Ilori, ta ce akalla mutum miliyan 1.6 ne daga cikin mutane miliyan biyu dake fama da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV, ke karbar magani a Nijeriya.
Dr Temitope Ilori, ta ce wannan cutar ta fi kama wadanda ke tsakanin shekaru 15 zuwa 65, kuma karfin yaduwarta a kasar yana kashi 1.4
Ta bayyana hakan ne a wurin wani taro da aka shirya gabanin bukin ranar yaki da cutar AIDS da ya gudana a Abuja.
An ware ranar 1 ga watan Disamban kowace shekara ne domin wayar da kan al'ummar duniya akan irin hadarin wannan cutar tare da karfafawa wadanda ke rayuwa da wannan cutar mai karya garkuwar jiki.