Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya Dr Bello Matawalle ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Laftanal Janar Taoreed Lagbaja da Allah Ya yi wa rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya. Janar Taoreed Abiodun Lagbaja dai shi ne babban hafsan sojin kasa na Nijeriya na 23.
A cikin wata sanarwa daga mataimaki na musamman kan harkokin kafafen yada labarai ga Ministan, Ahmad Dan-Wudil, ta ce ministan ya isa gidan marigayin da ke Flag Staff House da ke Niger Barrack Abuja.
A yayin ziyarar, Dr Bello Matawalle ya tarar da Mrs Mariya Lagbaja da sauran 'yan'uwa da abokan arziki da suke taya iyalan jimamin wannan rashi, inda shi ma ya yi tasa ta'aziyyar.
Kazalika, Dr Matawalle ya tuno irin gudunmuwa da jajircewar marigayi Janar Lagbaja, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai kwazo, himma da jajircewa don ganin tsaron Nijeriya ya inganta.
"Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya sadaukar da rayuwarsa don samar da zaman lafiya a kasar nan, inda ya kasance abin koyi ga masu tasowa".
A shekarar 2023 ne dai shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada marigayi Janar Taoreed Lagbaja a matsayin babban hafsan sojin kasa na Nijeriya wato Chief of Army staff. Abokan aikinsa dai na matukar mutunta shi duba da salon tafiyar da jagorancinsa da himmarsa wajen inganta tsaron kasa.