Pep Guardiola |
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City za ta sanar da sabuwar yarjejeniya da kocin kingiyar Pep Guardiola.
Yarjejeniyar da aka cimma zata kai har zuwa watan Yunin shekarar 2026,kuma za a iya tsawaitata har zuwa shekarar 2027.
Pep Guardiola da mahukuntan kungiyar sun cimma matsaya tare da shirya takardu domin rattaba hannu kan yarjejeniyar.