Majalisar wakilan Nijeriya ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin babban hafsan sojin kasar.
Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta tantance Oluyede a jiya Laraba.
Tun da farko an nada Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin mukaddashin babban hafsan soji bayan rashin lafiyar Laftana Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ta tsananta wanda ya rasu 5 ga watan Nuwamba.
Category
Labarai