Majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da kirkiro gundumomi 8 a jihar


Majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da kirkiro wasu gundumomi 8 a karkashin masarautar Katsina da Daura dake jihar.

A zaman majalisar na yau Laraba karkashin jagorancin Kakakin majalisar Alhaji Nasir Yahaya-Daura, a ka amince da wannan ya zama doka.

Gwamna Dikko Radda wanda ya aikawa majalisar kudirin dokar, ya ce kirkiro da wadannan gundumomi zai kara inganta harkar mulki ta hanyar baiwa sarakunan gargajiya taka rawa wajen samar da ci gaba tare da kai gwamnati kusa ga al'umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp