Majalisar dattawa ta amince da kudurin dokar garambawul ga haraji da ya janyo cece-kuce a cikin kasar, domin yin karatu na biyu.
Kudurin dokar wanda Shugaba Tinubu ya aikawa majalisar, ya tsallake karatu na farko bayan muhawarar da sanatoci su ka gudanar.
A 'yan kwanakinnan gwamnonin arewa da sarakuna da dattawan arewa sun yi fatali da wannan kudurin, bisa dalilin cewa gyaran bashi da wani amfani a daidai wannan lokaci.
Category
Labarai