Majalisar dattawa ta tsige shugaban kotun da’ar ma’aikata, Danladi Umar, bisa zarginsa da aikata ba daidai ba

Danladi Umar

Sun yanke wannan hukunci ne bisa dogaro da sashe na 157(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya wanda aka yi wa kwaskwarima,wanda ya baiwa majalisar dattawa ikon tsige wasu manyan jami’an gwamnati a tsarin doka.


Tsigewar ta biyo bayan zaman tattaunawa da 'yan majalisar suka yi wanda ya dauki tsawon awa daya da rabi.


Bayan dawowa zaman majalisar, majalisar dattawa ta sanar da cewa sama da ‘yan majalisa 84 ne suka goyi bayan matakin tsige shugaban.


Sanata Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da kudirin da ya kai ga tsige shugaban hukumar Danladi Umar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp