Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaba Tinubu na ciwo bashin ₦1.77tr

 

Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaba Tinubu na ciwo bashin ₦1.77tr 


Majalisar dattijai ta Nijeriya ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ya ciyo bashin Naira tiriliyan 1.77, kwatankwacin naira biliyan 2.2 domin cike gibin kasafin kudin 2024.


Wannan na zuwa ne bayan bayan da aka kada kuri’ar amincewa da bukatar, a zaman majalisar wanda mataimakin shugaban majalisar Barau Jibrin ya jagoranta. 


Majalisar ta amince da wannan bashin ne bayan karɓar rahoton kwamitin kula da basukan gida da waje karkashin jagorancin Sanata Wammako Magatarkada. 


Shugaban kasar ya mika bukatar ne a ranar Talata, domin cike wani bangare na gibin kasafin kudin shekarar 2024 da ya kai naira Tiriliyan 9.7.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp