Wani sabon rahoton majalisar dunkin duniya ya nuna cewa mata da yara mata 85,000 ne ake kashe da gangan a cikin shekara ta 2023, kuma sama da shi 60 na matan mazajensu ne ko 'yan uwansu ke kashe su.
Wannan kididdigar na nuni da cewa, duk minti 10 ana kashe mace 1 babba ko yarinya, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.
Rahoton wanda ke zuwa a daidai lokacin da ake bukin kwanaki 16 na yaki da jin zarafin mata, ya bayyana irin hadari da kuma barazanar da mata ke fuskanta a duniya musamman a nahiyar Afrika.