Ma'aunin tattalin arziki GDP na Nijeriya ya karu da kashi 3.46 - hukumar kididdiga NBS


Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce ma'aunin tattalin arzikin Nijeriya ya karu zuwa kashi 3.46 a rubu'i na uku na shekarar 2024, inda ya kai naira tiriliyan 71.1.

Wani bayani da Shugaban hukumar kididdiga ta kasa Prince Adeyemi Adeniran Adedeji, ya ce an samu ci gaba da kashi 0.92 idan aka kwatanta da rubu'i na uku na shekara ta 2023 da ma'aunin GDP ya kai kashi 2.54.

Bayanin ya kara da cewa ma'aunin a rubu'i na uku ya yi sama da kashi 0.27 idan aka kwatanta da rubu'i na biyu na wannan shekara ta 2024.

Wannan ci gaban da aka samu, hukumar kididdiga NBS ta alakanta shi da ci gaban da aka samu fannin noma da kasuwanci da sadarwa da kuma harkar gidaje.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp