Sabuwar kungiyar 'yan bindiga da ake kira da Lakurawa ta hallaka mutane 15 tare da kore shanun makiyaya sama da 100 a karamar hukumar Augie da ke jihar Kebbi
Wani fitacce kuma mazaunin garin, Alhaji Bashir Isah Mera (Yariman Mera), ne ya bayyana haka yayin da yake tabbatar wa jaridar DailyTrust
ya ce ‘yan kungiyar sun mamaye garin ne a daidai lokacin da jama’a ke shirin Sallar Juma’a tare da kwashe shanu sama da
100.