Jigo a jam’iyyar NNPP Injiniya Rabi'u Kwankwaso ya bukaci masu rike sa madafun iko a Nijeriya su gaggauta magance halin matsi da 'yan kasa suke ciki
Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Asabar a gidan gwamnan jihar Abia, Alex Otti
Inda ya bayyana rashin tsaro, da tabarbarewar tattalin arziki, da yadda ake samun koma-baya a fannin ababen more rayuwa,
Ya je jihar Abia ne domin jajanta wa Gwamna Otti bisa rasuwar gwamnan farar hula na farko na jihar, Dr. Ogbonnaya Onu da ya rasu