Kungiyar manyan likitoci tare da likitocin hakora na Nijeriya sun tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai daga ranar Litinin dinnan

Likitoci


Lamarin da ake fargabar zai iya janyo tsayawar aiki a  kusan cibiyoyin kiwon lafiya 83, da kuma makarantun kiwon lafiya 64 a fadin kasar, kamar yadda shugaban kungiyar na kasa Farfesa Muhammad Muhammad wanda ya bayyana a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch. 


A cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata, ta ayyana cewa za ta shiga yajin aikin gargadi ne saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun kungiyar.


Yajin aikin ya soma a dukkan jami’o’i da manyan asibitocin Nijeriya daga Litinin 17 ga wata, zuwa Lahadi 24 ga watan Nuwamba, 2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp