Kungiyar likitocin Nijeriya reshen jihar Kano, ta ba da wa'adi ga gwamnatin jihar da ta gaggauta korar kwamishiniyar jin kai, Amina Abdullahi, sakamakon cin zarafin wata likita.
A wata sanarwa da shugaban Kungiyar, Dr. Abdurrahman Ali da Sakatare, Dr. Ibrahim D. Muhammad suka sanya wa hannu, kungiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Nuwamba a sashin kula da kananan yara na asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
A cewar sanarwar, an yi zargin Kwamishinar da mukarrabanta da jami’an tsaro suka ci zarafin likitar.
Zargin cin zarafin dai ya samo asali ne sakamakon rashin samun magungunan da aka rubuta wa marasa lafiya, yayin da ta ke kula da marasa lafiya sama da 100.
Biyo bayan wannan al'amari, kungiyar Kano ta yi barazanar dakatar da aikin jinya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad cikin sa’o’i 48, idan ba a biya musu bukatunsu ba.