Kungiyar nan mai sanya ido kan harkokin aikin hajji a Nijeriya "Independent Hajj Reporters" ta yi kira ga hukumar alhazzai ta kasa NAHCON da ta kafa wani kwamiti na musamman da zai san ya ido akan aikin mayarwa mahajjata 95,000 da suka yi aikin hajji a shekara ta 2023 kudaden su.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Ibrahim Muhammad, ya ce wannan ya zama tilas domin magance duk wasu korafe-korafe da ke biyowa bayan an mayar da kudade.
A saboda haka shugaban kungiyar Ibrahim Muhammad ya bukaci NAHCON ta fitar da bayanan kudin da ta tura, kuma ta tilastawa hukumomin bayyana yawan mutanen da za a mayarwa kudaden tare da kafa wani kwamiti da zai kunshi har da 'yan jarida da zai tabbatar da cewa an biya mahajjatan hakkokinsu.
Category
Labarai