Shugaban IPMAN na kasa Abubakar Garima wanda ya sanar da hakan a Abuja, bayan kammala taron shugabannin kungiyar, yace an samu wannan ci gaba ne bayan tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
Abubakar Girima ya yi amannar cewa wannan yarjejeniya zata kara taimakawa wajen samun wadataccen mai a fadin kasar.
Dangane da farashi kuwa, Shugaban na IPMAN ya nuna kwarin gwuiwar cewa tattaunawar da suke yi da matatar Dangote za ta haifar da da mai ido.