Kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta dakatar da babban jami’i a kungiyar Mamman Mike Osuman bisa furta kalamai a madadinta ba tare da an umurce shi ba kamar yadd jaridun Punch da Daily Trust suka ruwaito.
Wata takarda dauke da sa-hannun shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu, ta ce Kungiyar ta ACF ba ta ji dadin kalaman ba domin jami‘inta ya furta su ne bisa radin kansa cewa arewa ba za ta zabi wani dan takara wanda ba daga yankin ya fito ba a 2027 ba tare da ya tuntubi matsayar sauran jami‘an kungiyar ba.