Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun, ya ce kananan yaran da suka suma a kotu kafin a gurfanar da su a gaban kuliya, sun yi hakan ne da gangan.
An kama masu zanga-zangar #Endbadgovernance a Nijeriya cikin watan Agusta inda ake ci gaba da tsare su a Abuja domin gurfanar da su a gaban kotu.
A Juma'ar makon nan ne aka ga matasan a cikin wasu hotuna da ke nuna su a yanayi marar kyau sakamakon yadda ake tsare da su