Mukaddashin babban hafsan sojojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya umurci dakarun soji da su murkushe sabuwar kungiyar yan ta'adda wadda ta bulla a jihohin Sakkwato da Kebbi mai suna Lakurawa.
Olufemi ya bayar da wannan umurni ne a lokacin ziyarar da ya kai hedikwatar runduna ta 8 dake Sakkwato, kwanaki kadan bayan hedikwatar tsaro ta fitar da rahoton bayyanar sabuwar kungiyar.
A yayin ziyarar da ya kai a karamar hukumar Tangaza, daya daga cikin kananan hukumomin da yan bindigar ke ta'adi, mukaddashin babban hafsan ya bukaci al'umma su baiwa jami'an tsaro bayanai domin samun nasara a yakin da suke da matsalar tsaro.