Kotu ta wanke Kwamishinan Jigawa da aka zarga da aikata lalata da matar aure
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano, karkashin jagorancin Ibrahim Sarki Yola, ta wanke Auwal Danladi Sankara, Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa daga zargin aikata zina da wata matar aure.