Kotun tarayya dake Abuja ta dage sauraren karar da hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta shigar akan tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello har sai ranar 13 ga watan Disamba 2024.
Mai Shari'a Emeka Nwite ta dage zaman ne bayan da a farko ta dage sauraren karar har sai 21 ga watan Janairu 2025.
Sai dai lokacin da aka tambayi Yahaya Bello lauyansa, ya shaidawa an sanar da shi zaman kotun ne cikin dare hakan ya sa bai samu damar kiran lauyoyinsa ba.
Sai dai alkalin kotu ya umurci EFCC ta ci gaba da tsare shi kuma ta sanar da lauyoyinsa ranar 13 ga watan Disamba da kotun za ta sake zama.