Kotu ta dakatar da hukumar tace fina-finai ta Kano daga tuhumar Rarara



Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta dakatar da hukumar tace fina-finai ta jahar Kano daga tuhumar mawaki Rarara kan zargin da take mishi na laifin sakin waka ba tare da ta sahale masa ba.

Jami'in yada labarai na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya tabbatar da cewa kotun ta kuma dakatar da hukumar daga daukar wani mataki har sai an kammala sauraren karar da ya shigar a gabanta.

Idan ba a manta ba tun a makon da ya gabata ne hukumar tace fina-finai ta jahar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha ta shigar da mawakin kara a wata kotu da ke jahar bisa zargin sa da laifin yin gaban kansa wajen yin waka tare da sakinta ba tare da kaiwa hukumar ta tantance ba.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp