Mai shari'a Maryanne Anenih ta kotun babban birnin tarayya Abuja, ta bada umurnini ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a hannun hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Alkaliyar kuma ta dage shari'ar har sai 10 ga watan Disamba 2024 domin yanke hukuncin akan bukatar bayar da shi beli.
An gurfanar da Yahaya Bello ne tare da wasu mutane biyu; Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu, akan zarge-zarge 16 wadanda suka musanta aikatawa.
Category
Labarai