Hashimu Dungurawa da Kawu Sumaila |
Shugaban jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Hashimu Dungurawa, na fuskantar barazanar gurfana gaban shari’a kan wasu kalamai da ya yi kan Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, AbduRahman Kawu Sumaila a kwanakin baya.
Shugaban jam’iyyar ya zargi sanatan da karkatar da sama da dala miliyan 80 da aka ware domin gudanar da ayyukan mazabu.
Kawu Sumaila ya bukaci shugaban jam'iyyar NNPP na Kano da ya janye kalamansa kuma ya nemi afuwa, ko kuma ya dauki matakin shari'a, a cewar wata wasika da lauyansa Barista Sunusi Musa ya sanyawa hannu
Daga cikin zarge-zargen da Hashimu Dungurawa yayi, har da zargin Kawu Sumaila da karkatar da kudaden da aka tanada domin gudanar da gina filin wasa a karamar hukumar Sumaila lokacin da yake dan majalisar wakilai, tare da karbar dala miliyan 80 daga hannun Abubakar Kabiru Bichi don yin magudin zaben gwamnan Kano a shekarar 2023.