Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya tafi kasar Côte d’Ivoire domin halartar wani taro kashashe kan harkar makamashi na shekara ta 2024.
Taron zai gudana ne daga ranar 27 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamban 2024 a birnin Abidjan.
Sanarwar da mai taimawaka Kashim Shettima kan yada labarai Stanley Nkwocha ya fitar, ta ce Mataimakin shugaban ya amsa gayyatar da Mataimakin shugaban kasar Côte d’Ivoire, Tiémoko Meyliet Koné ya yi masa domin halartar taron.
Category
Labarai