Kanin Kwankwaso ya maka Abba Gida-gida a kotu - Jaridar Daily Nigerian

 



Garba Musa Kwankwaso shi ne shakiki ga tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da ya maka Abba Gida Gida a kotu 


Takaddammar ta taso ne tun zamanin mulkin Rabiu Musa Kwankwaso lokacin da shi tsohon gwamnan, Kwankwaso, ya karbi filayen a hannun wasu tare da mallaka shi ga kamfanin WAECO NIGERIA LIMITED, kamfanin da jaridar Daily Nigerian ta ce bayanan sun nuna shi da kansa da kaninsa Garba na cikin daraktocinsa 



Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Kwankwaso ya karbi filayen a hannun mutanen ba tare da biyan su diyya ba, lamarin da ya sa suka garzaya hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe korafe ta jihar Kano a zamanin mulkin Ganduje. 


A shekarar 2017, lokacin da yake shugaban hukumar karbar korafe-korafen, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya karbi korafin tare da rubuta wa tsohon gwamna Ganduje korafin mutanen.



Bayanan gudanar da bincike , gwamna Ganduje ya kwace filin daga kamfanin WAECO tare da mayar da shi ga masu ciki har da iyalan attajiri Dantata, lamarin da bai yi wa daraktocin kamfanin dadi ba.


Rahotan jaridar Daily Nigerian ya gano cewa bayan da Abba Gida Gida ya yi nasarar zama gwamnan Kano, kamfanin WAECO karkashin jagorancin Garba Musa, Ddan uwa ga jagoran Kwankwasiyya Rabiu Kwankwaso, ya bukaci Abba ya kwato filayen daga hannun mutanen ya dawo masa da mallakin filin. Sai dai jaridar Daily Nigerian ta gano cewa Gwamna Abba bai yi na‘am da wannan bukata ba, matakin da ya hassala Garba Kwankwaso ya ga dacewar gurfanar da gwamnan tare da wasu mutane a gaban kotu.



A yanzu, dan uwan na Kwankwaso na fatan kotu ta tilasta wa gwamna Abba ba shi wannan fili tare da haramta wa mutanen ci gaba da amfani da filin da ke rukunin gidaje na Kwankwasiyya City a cikin birnin Kano.


A ranar 27 ga watan Nuwamba ne dai ake sa ran za a ci gaba da sauraron wannan kara a gaban alkali Usman Na'abba. 


Gwamnan Kano da kwamishinan kasa da tsara birane da hukumar tsara birane ta jihar Kano da atoni-janar na jihar Kano da kuma wasu mutane da ba a bayyana sunayensu ba, sune Alhaji Garba Musa ya maka kotu domin a biya masa bukatunsa, kamar yadda takardar shigar da karar da aka rattaba hannu a kanta a ranar 18/07/2024 ta nunar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp