Katafaren kamfanin mai na Oando a Nijeriya ya bayyana cewa ya samu ribar Naira biliyan 60.3 a cikin shekarar 2023 da ta gabata.
Kamfanin ya samu karuwar kudaden shiga da kashi 43%, inda ya kai Naira tiriliyan 2.9 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 1.9 a shekarar 2022 kamar yadda Daily trust ta rawaito.