Kada ka saryantar da amanar Kanawa da ke kanka, saboda yi wa Kwankwaso biyayya - Kawu Sumaila ya ja hankalin Gwamna Abba na Kano


Sanata mai wakiltar yankin Kano ta Kudu, Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya shawarci gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf cewa, kada ya juyawa Kanawa baya domin yi wa tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa biyayya. 


A wata ganawa da manema  labarai a Abuja, Sanatan ya ce Gwamnan ba zai iya da alhakin miliyoyin al'ummar jihar ba idan ya juya musu baya. 


A cewar Kawu Sumaila dole ne Gwamna Abba ya hada kai da mai gidansa Kwankwaso domin ci gaban al'ummar Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp