Jirgin ruwa dauke da mutane sama da 200 ya kife a jihar Neja


Wani mummunan hadarin jirgin ruwa da ya faru da sanyin safiyar yau Juma'a a yankin Dambo-Ebuchi na jihar Neja ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

Wani shaidun gani da ido ya ce jirgin ya dauki mutane da suka kai 200 ciki har da mata da 'yan kasuwa dake kan hanyar zuwa kasuwar Katcha dake ci mako-mako.

Rahotanni sun ce masu aikin ceto na ci gaba da kokarin ceto mutanen da jirgin ya kife da su, kuma zuwa yanzu an tsamo gawar mutum 8, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp