Jam'iyyun YPP da ZLP sun bada mamaki a zaben kananan hukumomi a Abia
Jam’iyyar Labour Party a jihar Abia ta Gwamna Alex Otti ta sha kaye a zaben kananan hukumomin da aka gudanar ranar Asabar.
Sabbin Jam'iyyu irinsu; Young Progressive Party da Zenith Labour Party su suka yi kaka gida a zaben
Jam'iyyar ta LP ba ta samu damar lashe koda kujera daya ba, jam'iyyar Zenith Labour Party, ZLP ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi 15 yayin da YPP ta samu kujeru biyu.
Haka kuma sanannun jam'iyyu da suka hada da APC, PDP da kuma NNPP su ma ba su samu karbuwa ba
a zaben