Jam'iyyar ACCORD ta kori wanda ya yi mata takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata
Shugaba da Sakataren jam'iyyar na kasa Barrister Maxwell Mgbudem da Dr. Adebukola A. Ajaja, ne suka sanar da korar Professor Christopher Imumolen, bisa samunsa da laifin cin dunduniyar jam'iyyar wato "Anti Party".